Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a Jihar Edo, ta bayyana cewa, daga cikin katin zabe na dindindin 30,979 (PVC) da ke shirin karba a jihar, ya zuwa yanzu 1,348 ne kawai aka karba.
Jami’in hukumar mai kula da wayar da kan masu kada kuri’a, Timidi Wariowei ne ya bayyana hakan a karshen mako a Benin yayin da yake zantawa da manema labarai kan ci gaba da rijistar masu kada kuri’a a jihar.
Wariowei ya ce, “Tun daga watan Janairun 2022, muna da jimilar Katin Zabe na Dindindin 30,979 don rabawa da karba. Amma daga cikin wadannan lambobin, PVC guda 1,348 ne kawai masu su suka karba.”
Ya koka da cewa tarin ba abin karfafa gwiwa ba ne, don haka ya yi kira ga jama’a da su zo su karbi katin zabe domin kada kuri’a a zaben 2023 mai zuwa.