A hukumance kawo yanzu, shugaban hukumar zaɓe INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya karɓi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na jihohi huɗu.
Jihohi huɗun da aka gabatar da sakamakonsu a zauren taron sun haɗar da Ekiti da Kwara da Osun da kuma Ondo.
Sakamakon dai ya nuna dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a jihohi uku watau Ekiti da Kwara da kuma Ondo.
A yayin da shi kuma dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zabe a jihar Osun.
An samu hayaniya a cikin zauren tattara sakamakon zaben bayan da wadansu jam’iyyu suka ki amincewa da sakamakon zaben na jihar Ekiti.
Hukumar INEC ta tafi gajeren hutu sai bayan sa’a daya za ta dawo.