fidelitybank

INEC ta gayyaci shugabannin APC da na PDP a kan farwa juna

Date:

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu, ya gayyaci shugabannin jam’iyyu don yin zama kan rahotannin far wa juna da magoya bayansu suka yi a wasu jihohi.

Yakubu ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin wani shiri na horar da jami’an zabe kan amfani da na’urorin zamani a zabukan 2023 da ke tafe a cikin kasar, inda kuma ta ce ‘yan sandan kasar za su kashe kudi naira biliyan 13 domin sayen makamai gabannin zabukan.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa far wa juna da magoya bayan jam’iyun suka yi na zuwa ne makonni uku da soma yakin neman zabe da kuma sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan takarar shugaban kasa suka yi karkashin jagorancin kwmaitin samar da zaman lafiya ta kasa.

Kafin soma yakin neman zabe a ranar 28 ga watan Satumba, an yi ta samun cacar baka tsakanin magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da kuma na jam’iyyar Labour, Peter Obi.

Wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta wanda ya nuna mambobin wata kungiya na zagin dan takarar shugaban kasa na gaba-gaba ya janyo fushi da kuma Alla-wadai a fadin kasar.

Kafin faruwar lamuran, ‘yan sanda sun gargadi ‘yan siyasa da magoya bayansu kan yin kalaman kiyayya da kuma cin zarafi a intanet, inda ta yi barazanar hukunta wadanda aka samu da laifi.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar Æ´ansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na É—aya daga cikin jhihohin da ake kaÉ—a...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...
X whatsapp