Hukumar zabe ta kasa INEC, da hukumar da ke sa ido kan kafofin watsa labarai ta NBC da sauran masu ruwa da tsaki a kan lamarin zabe sun gudanar da wani taro a Abuja, babban birnin kasar.
Shi dai wannan taron an yi shi ne da zummar jawo hankalin jamâiyyun siyasa da kafofin watsa labarai don ka da su bari a yi amfani da su wajen halasta kudin haram a lokacin zaben 2023.
Taron na masu ruwa da tsaki kan maganar kawar da yin amfani da kudi a zabe mai zuwa ya kunshi bangarori daban-daban.
Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahamud Yakubu, ya ce sun cimma daidaito a tsakanin dukkan mahalarta taron.
Wasu dai daga bangaren mahalarta taron sun yi korafi kan maganar kayyade fitar da kudi daga asusun banki duk rana da babban bakin Najeriya ya sanar.