Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar Edo ta yi kira ga hukumar zaɓen ƙasar da ta bayyana sakamakon zaɓen da ke kan na’urorin adana sakamakon zaɓe na hukumar wato IREV.
Gwamnan jihar Gowdin Obaseki da takwarorinsa na jihohin Adamawa da Taraba ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai da suka gabatar a ɗakin tattara sakamakon zaɓe na jam’iyyar wato ‘ PDP Situation Room’.
Gwamnonin uku sun zargi hukumar INEC da rubuta sakamakon da ba na gaskiya ba a kan takardar rubuta sakamakon a wasu rumfunan zaɓen jihar.
Tuni dai hukumar zaɓen ta ce ta ƙaddamar da bincike kan zargin rubuta sakamakon bogin a kan takardun rubuta sakamakon zaɓen.
Sannan ta buƙaci a kwantar da hankala da bin doka da oda da mutunta juna yayin da take dab da fara aikin karɓar sakamakon.