fidelitybank

INEC ta fara rabon katin zaɓe na shekarar 2023

Date:

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce, ta fara raba katinan zabe na dindindin guda 23,871 ga sabbin masu rajista a jihar Gombe.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mohorret Bigun ya fitar ranar Alhamis a Gombe.

Bigun ya ce, PVCs 23,871 da aka karba na wadanda suka yi rajista ne ko kuma suka nemi sabunta bayanai, canja wuri ko maye gurbin katunan da suka bata ko lalace.

A cewar sa, an raba ne ga wadanda suka yi rajista a zangon farko da na biyu na shirin ci gaba da rijistar masu kada kuri’a (CVR) da ake gudanarwa tsakanin ranakun 28 ga watan Yuni zuwa 20 ga Disamba, 2021.

“Saboda haka, duk wadanda suka yi rajista ko suka nemi a maye gurbinsu da PVC a lokacin, ana karfafa su da su ziyarci ofisoshin INEC da ke fadin kananan hukumomin inda rumfunan zabe ke zaune don karbar PVC daga ranar Alhamis 21 ga Afrilu, 2022.”

Ya kuma ba da tabbacin wadanda suka yi rajista a rubu’in farko na shekarar 2022 da kuma wadanda ake gudanar da aikin a yanzu cewa za a yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a kafin zaben 2023.

Bigun ya yi kira ga ‘yan Najeriya da suka cancanci shekaru 18 zuwa sama, da su yi rajista.

current eggon news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp