Hukumar zaɓe ta INEC, ta fara raba kaya da ma’aikatan da za su gudanar da zaɓen gwamna da ‘yan majalisar dokoki a jihar Kaduna.
Hukumar ta ce, ta na ganin hakan ya zama wajibi ne da ɗauki wannan matakin na shirya wa zaɓukan da wuri, inda ta fara aika muhimman kayan daga Babban Bankin Ƙasar inda aka ajiye su zuwa ƙananan hukumomin jihar 23.
A ranar Asabar ne za a yi zaben Gwamna da na ‘yan majalisar jihohi.