fidelitybank

INEC ta dakatar da yin rijistar zaɓe a Enugu

Date:

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta dakatar da aikin rajistar masu kada kuri’a a karamar hukumar Igboeze ta Arewa da ke jihar Enugu, sakamakon harin da aka kai wa ma’aikatanta a yankin.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an hukumar da ke gudanar da rijistar zabe tare da kona ofishinta a yankin Igboeze ta Arewa.

Duk da cewa ba a samu asarar rai ba, akwatunan zabe 748, dakunan zabe 240, kayan ofis da kayan aiki sun lalace.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wata sanarwa da Festus Okoye, kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ya fitar.

A cewar sanarwar da INEC ta fitar, Jude Okwuonu, sakataren gudanarwa a Enugu, ya ruwaito cewa, an kai harin ne da misalin karfe 2:30 na ranar Laraba a makarantar Community Primary School Umuopu da ke Umuozzi mazaɓa 19 a karamar hukumar Igboeze ta Arewa.

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp