fidelitybank

INEC ta dakatar da ma’iakatan masu sakaci da aikin su

Date:

Hukumar Zaɓe inec, ta dakatar da dukkan ma’aikatan da aka samu da sakaci lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar asabar da ta gabata 25 ga watan Fabirairu.

INEC ta ce dukkansu ba za su yi aikin zaɓen da za a yi ba na ‘yan majalisar jiha da na gwamnonin a ƙasar da za a yi a ranar 11 ga watan Maris.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da kwamishinonin zaɓe a ranar Asabar a Abuja.

“Yayin da muke tunkarar zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jiha, dole mu ƙara ƙoƙari domin shawo kan matsalolin da muka fuskanta a zaɓen da ya gabata. ‘Yan Najeriya ba za su yarda da wani abu ba bayan wannan.

“Dukkan ma’aikacin da aka samu da sakaci, ma’aikacin INEC ne ko kuma na wucin gadi ne, cikin harda masu tattara sakamako da turawan zaɓe to ba za mu kyale su yi aikin zaɓen mai zuwa ba.

“Dole kwamishinonin zaɓe su ɗauki matakan da suka dace a wuraren da aka samu hujjojin cewa an yi abubuwa ba daidai ba,” in ji Farfesa Mahmood.

naija news today legits

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp