Huhukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, ta ce nan ba da jimawa ba za ta buɗe wani shafin da zai bai wa ƙungiyoyin da ke neman zama jam’iyyu damar bayyana aniyarsu gare ta.
Hakan na cikin matakan da hukumar ke bi domin rajistar sabbin jam’iyyu gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.
Tuni dai wasu ƙungiyoyin da suka riga suka miƙa wa hukumar buƙatarsu a rubuce suka zargi INEC ɗin da yi masu zagon ƙasa ta hanyar jan ƙafa wajen yi musu rajista, zargin da hukumar ta musanta.
Zainab Aminu Abubakar, jami’a a ɓangaren watsa labarai na hukumar zaɓen ce ta yi wa BBC wannan jawabin kan kan matakin da hukumar take ɗauka a yanzu game da aikin rajistar sabbin jam’iyyun.