Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce za ta rubuta wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Baba Ahmed, domin ya yi bincike tare da gurfanar da Hudu Yunusa Ari, Kwamishinan Zabe (REC) na Adamawa.
Matakin ya biyo bayan taron fasaha na ranar Talata wanda kwamishinonin hukumar zabe na kasa suka halarta a Abuja.
Hukumar ta kuma bayyana cewa za a ci gaba da tattara sakamakon zaben ne a daidai lokacin da jami’in tattara sakamakon zaben ya tantance.
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, INEC ta ce ta kuma yanke shawarar rubutawa sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha, domin ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayani game da “halayen da ba su dace ba” na REC.
Sanarwar ta kara da cewa: “A taron da ta yi a yau, 18 ga Afrilu, 2023, Hukumar ta tattauna batutuwan da suka taso daga zaben Gwamnan Adamawa inda ta yanke shawarar: