Shugaban hukumar zabe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana shirye-shiryen sahihancin zabukan 2023 duk da rashin tsaro.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bukaci jam’iyyun siyasa da su mika kwafin rajistar mambobinsu ga hukumar kafin zabensu na farko.
Hukumar ta ce, umarnin ya yi daidai da sabuwar dokar zabe ta 2022, da kuma wajibcin da doka ta tanada.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a taron koli karo na biyu na duk wata uku na kwamishinonin zabe a Abuja jiya.
Ya kara da cewa, ayyukan da ke cikin jadawalin da jadawalin ayyuka na babban zabe na 2023 sun tsaya tsayin daka, ya kuma shawarci masu ruwa da tsaki da su yi la’akari da hakan wajen tsara ayyukansu.
Yakubu ya bayyana cewa, kimanin jami’an zabe miliyan daya, na yau da kullum da na wucin gadi, za a tura runfunan zabe 176,846 a mazabu 8,809 da kuma kananan hukumomi 774 na kasar nan.