Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, ta aike wa Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan sanarwa a hukumance kan koken da ƴan mazaɓarta suka kai na ƙoƙarin yi mata kiranye daga majalisa.
INEC ta kuma tabbatar da samun cikakkun lambobi da adireshin wakilan da suka tura koken da takardun sanya hannu kan batun yi mata kiranye.
Wakilan sun aika bayanan nasu masu muhimmanci ne cikin wata wasiƙa ga shugaban hukumar.
A cewar ƴan mazaɓarta, suna ƙoƙarin yi wa sanatan kiranye ne saboda ba ta wakiltar su yadda ya kamata.
Tun a baya INEC ta bayyana cewa a shirye ta ke ta bi matakan da kundin tsarin mulki ya shimfiɗa mata na yin irin wannan kiranye da zarar masu ƙorafin sun cika ƙa’idojin da doka ta gindaya.
Sanata Natasha dai na fuskantar kiranye ne tun bayan taƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da shugaban majalisar dattijan Najeriya Godswill Akpabio bayan ta zarge shi da yunƙurin cin zarafi na lalata.