fidelitybank

INEC ta ƙara tura inji 209 na rijista zuwa Jihohin Kudu maso Gabas guda biyar da Legas da Kano

Date:

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta tabbatar da karuwar bukatar rajistar masu zabe.

Festus Okoye shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ya fitar da sanarwa a ranar Juma’a.

Jami’in ya ce, rahotannin da ake samu daga jihohin sun nuna cewa, an samu karuwar aikace-aikacen da ba a taba yin irinsa ba da kuma kalubalen da ‘yan kasar ke fuskanta.

Ya yi nuni da cewa, dukkan kwamishinonin zabe (RECs) sun yi taro a ranar Alhamis domin duba lamarin.

Okoye ya sanar da sakin karin injuna 209 zuwa Jihohin Kudu maso Gabas guda biyar da Legas da kuma Kano, inda matsalar ta fi kamari.

Alkalan zaben dai sun yi alkawarin sanya ido kan lamarin nan da ‘yan kwanaki masu zuwa tare da sake ganawa, domin duba yadda aikin ke gudana.

INEC ta kara da ba da tabbacin cewa, za a bi duk wani mataki na bai wa ‘yan Najeriya da suka cancanta damar cin gashin kansu. In ji Daily Post.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kowane dan Najeriya da ya kai shekaru 18 zuwa sama yana da ‘yancin yin rajista da zabe a duk fadin kasar da yake zaune ba tare da wata tsangwama ba”.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp