Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi ƙarin bayani dangane da ƙungiyoyi 25 da suka nemi ta musu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa a ƙasa gabanin zaɓukan 2027.
Hukumar zaɓen ta INEC ta ce nan gaba tana sa ran samun ƙarin wasu ƙungiyoyi da ka iya gabatar da tasu buƙatar kasancewar ta kan sami hakan duk bayan zaɓe.
Zainab Aminu, mai magana da yawun hukumar zaɓen ta shaida wa BBC cewa, yi wa ƙungiyoyin siyasa rajista a matsayin jam’iyya ɗaya ne daga cikin ayyukan hukumar INEC matuƙar ƙungiyoyin sun cika ƙa’idojin da aka gindaya na zama jam’iyya.
Ta ce zuwa yanzu, INEC tana aiki kan buƙatun ƙungiyoyin kuma da zarar sun cika duka matakan, za a yi musu rajista a matsayin jam’iyyu.