Tsohon shugaban mataimakin shugaban kasa wanda kuma ya yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar, ya roƙi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC a jihar Adamawa ta ayyana Jam’iyyarsa da ɗan takararta Ahmad Umar Fintiri a matsayin waɗanda suka yi nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar.
Atiku ya shaida wa BBC cewa bisa alƙaluman da aka wallafa a shafin INEC, PDP ce kan gaba da APC wadda Aishatu Dahiru Ahmed Binani ke yi wa takara.
Karanta Wannan: Umar Bago ya lashe zaben gwamnan Neja a APC
A cewarsa, an gudanar da zaɓe lafiya ba tare da wata matsala ba, inda ya yi zargin cewa ana ƙoƙarin yin murɗiya saboda jan ƙafar da ake yi wajen sanar da sakamakon zaɓen ƙaramar hukuma ɗaya da ake taƙaddama kan sakamakonta.
Tuni dai hukumar INEC ta sanar da sakamakon ƙananan hukumomi 20 na jihar.
Atiku Abubakar ya ce rashin sanar da sakamakon ƙaramar hukumar Fufore a kan lokaci na iya haifar da illa ga zaman lafiyar jihar Adamawa.
A halin da ake ciki dai manyan jam’iyyun da ke fafatawa a zaɓen na iƙirarin samun nasara a zaɓen