Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a ranar Juma’a, ta bayyana cewa ba ta da masaniyar inda aka dakatad da kwamishinan zabe na reshen jihar Adamawa, Yunusa Hudu Ari.
A ranar Asabar din da ta gabata ne Ari ya haifar da cece-kuce a lokacin da ya ayyana Aisha Binani ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben cike gurbin kujerar gwamnan jihar Adamawa.
Ari dai ya ayyana Binani ne a matsayin wanda ya lashe zaben yayin da INEC ba ta kammala tattara sakamakon zaben ba.
Amma, INEC ta yi fatali da sanarwar Ari tare da sanar da Ahmadu Fintri a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kidaya sakamakon.
Sai dai mai magana da yawun hukumar ta INEC, Festus Okoye, ya ce Ari bai amsa kiran nasa ba tun lokacin da ya dauki wannan aika-aika.
Da yake bayyana a gidan Talabijin na Channels, Okoye ya ce: “Ba mu san inda yake ba, domin bayan faruwar wannan lamari, hukumar ta rubuta masa takarda kuma ta kira shi a waya.
“Bai taba mayar da ko daya daga cikin kiran ba; bai amsa ko daya daga cikin kiran ba.
“Mun nemi ya kai rahoto ga Hukumar ranar Lahadi, ba mu gan shi ba, mun ce ya kawo rahoto ranar Litinin, ba mu gan shi ba. Don haka har zuwa yanzu, bai bayar da rahoto ba kuma ba mu san inda yake ba.”


