fidelitybank

INEC maguɗi ta yi ta baiwa Tinubu – Kwankwaso

Date:

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya yi zargin cewa magudin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi, ya kai ga nasara ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Kwankwaso ya yi zargin cewa, INEC ta yi wa Tinubu kuri’u da magudi a zaben shugaban kasa da aka kammala.

A wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, Kwankwaso ya nuna cewa, ‘yan Najeriya ba sa son jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Ya ce jam’iyyar NNPP tana da makoma mai kyau domin “manyan ‘yan siyasa” na sha’awar jam’iyyar.

A cewar Kwankwaso: “Wani abu mai ban sha’awa shi ne yadda mutane da yawa musamman manyan ‘yan siyasa ke nuna sha’awarsu ga jam’iyyarmu, kuma a shirye suke su ba da gudummawar da suka dace don ciyar da jam’iyyar gaba. Ku kalli abokan hamayyarmu, musamman PDP.

“Suna cikin mawuyacin hali, musamman yadda ya shafi shugabanninta. A jihar Kano, wasu sun yi tunanin PDP za ta taimaka musu, ko za ta kawo musu canji, amma abin ya ci tura. Haka da APC.

“Duk wadannan kuri’u da kuke gani INEC ta ambata an yi magudi ne ga dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu. Gaskiyar ita ce, ’yan Najeriya ba sa son APC kuma, don haka jam’iyyarmu ce ke da gaba.”

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...
X whatsapp