Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce cire dan takararta, Cif Timipre Sylva daga jerin sunayen ‘yan takarar gwamna a zaben gwamnan Bayelsa a ranar 11 ga watan Nuwamba da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi.
Mista Felix Morka, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
“An jawo hankalin jam’iyyar APC kan sabunta jerin sunayen ‘yan takarar gwamna a zaben gwamnan Bayelsa da INEC ta yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, wanda ya cire sunan dan takararmu, Cif Timipre Sylva.
“Wannan matakin da INEC ta dauka ba zai rasa nasaba da hukuncin da babbar kotu ta yanke a ranar 9 ga watan Oktoba ba, wanda ya haramtawa Cif Timipre Sylva a matsayin dan takarar jam’iyyarmu.
“Dan takararmu da jam’iyyarmu ba tare da bata lokaci ba suka daukaka kara kan wannan hukunci tare da kawo wasu matakai na neman a dakatar da aiwatar da hukuncin.
“Da yake la’akari da tsananin gaggawar lamarin, kotun daukaka kara ta ba da umarnin hanzarta sauraron karar da aka sanya a ranar Juma’a 27 ga watan Oktoba,” in ji Morka.
Ya kara da cewa INEC na cikin lamarin kuma an ba ta dukkan takardu da umarni da suka dace dangane da lamarin.
Ya ce soke dan takarar APC a cikin yanayi kamar yadda INEC ta yi abu ne da bai dace ba a fili kuma yana iya tsara sakamakon daukaka karar da aka shigar a kan lamarin.
Ya ce cire dan takarar jam’iyyar daga cikin jerin sunayen ‘yan takarar gwamna a Bayelsa zai haifar da halin ko in kula a kotun daukaka kara, dan takara da jam’iyyar idan karar ta yi nasara.
Morka ya bukaci INEC da ta janye gyaran da ta yi bisa la’akari da yadda ake yin adalci.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Bayelsa, musamman jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar APC da magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu yayin da tsarin shari’a ya cika.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa dan takarar jam’iyyar zai yi nasara a kotun daukaka kara da kuma a rumfunan zabe.
Mai shari’a Donatus Okorowo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, a hukuncin da ta yanke a ranar 9 ga watan Oktoba, ta haramtawa Sylva takara a zaben gwamna da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Okorowo ya yanke hukuncin cewa Sylva da aka rantsar da shi sau biyu kuma ya yi mulki na tsawon shekaru biyar a matsayin gwamnan Bayelsa, zai karya kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima idan ya sake tsayawa takara.


