Firaministan India Narendra Modi, ya shiga jerin shugabanni da kuma ɗimbim alummar da ke miƙa ta’aziyyarsu bisa rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Modi ya jinjinawa kaifin basira da jajircewar marigayi tsohon shugaban ƙasar kan ƙarfafa alaƙar India da Najeriya a lokacin mulkinsa.
Ya kuma ƙara da cewa ” Na shiga matuƙar damuwa da rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.”
” Ina iya tuna tarukanmu da tattaunawarmu a lokuta da dama”
”Da ni da alummar India su biliyan 1.4, munna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da gwamnati da kuma mutanen Najeriya.” in ji shi.