fidelitybank

Ina zama shugaba zan cire tallafi man fetur – Tinubu

Date:

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin janye tallafin man fetur da zarar ya zama shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana haka ne ranar Alhamis da daddare a yayin da yake gudanar da taro da wasu ‘yan kasuwa.

“Dokar man fetur tana nan kuma za mu duba ta a karo na biyu domin sauke nauyin da ke kanmu kuma duk zanga-zangar da za a yi, za mu cire tallafin man fetur,” in ji Tinubu.

Ya kara da cewa: “Za mu dauki matakai masu tsauri, wannan shi ne batun gaskiya. Don haka wajibi ne mu cire tallafin man fetur.”

Tinubu ya kara da cewa zai sanya kudin da ake biyan tallafin man fetur a fannonin da suka kamata irin su lafiya.

Kazalika ya ce zai cire jerin haraje-haraje da hukumomi suke karba yana ma cewa zai sa a rika karbar haraji daya kan mu’amalar da ta shafi a biya mata haraji.

Bayanai sun nuna cewa gwamnatin Najeriya ta biya N1.9 daga watan Janairu zuwa watan Yulin 2022 kadai, lamarin da wasu ke ganin ba abu ne mai dorewa ba.

Da ma dai shi ma dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya dade da shan alwashin janye tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa. Ya ce tallafin ba ya yi wa talakawa amfani.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp