Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce batun da ake yaɗawa cewa yana ƙwace filaye ba haka ba ne, inda ya ce yaƙi yake yi da masu ƙwace filaye, ba shi yake ƙwacen ba.
Wike ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a wani taron da ƴan PDP na ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas na jihar Ribers, inda ya yi godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wike ya ce, “ina yaƙi ne da masu ƙwacen filaye. Wasu na cewa wai ƙwacen filaye ake yi, ta yaya za ka ƙwace filaye alhali kai ne ke da iko da filayen? ni nake da iko filaye a Abuja, to ta yaya zan ƙwace abun da nake da iko a kai?”
Ya ƙara da cewa yanzu ba kamar Rivers ba, da ƴan Najeriya baki ɗaya yake aiki, wanda hakan ya sa ƙara fahimtar wasu abubuwa.
“Wasu suna tunanin don ba a yi amfani da doka ba a baya, babu wanda zai zo ya yi. Amma ba haka ba ne, don wata gwamnati ba ta yi ba, hakan ba ya nufin babu gwamnatin ba za ta zo ta gyara. Don haka duk farfagandar da za a yi, ba za ta hana ni yin abubuwan da suka dace ba.”