fidelitybank

Ina yaƙi da masu ƙwacen filaye a Abuja ba ƙwace wa na ke yi ba – Wike

Date:

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce batun da ake yaɗawa cewa yana ƙwace filaye ba haka ba ne, inda ya ce yaƙi yake yi da masu ƙwace filaye, ba shi yake ƙwacen ba.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a wani taron da ƴan PDP na ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas na jihar Ribers, inda ya yi godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wike ya ce, “ina yaƙi ne da masu ƙwacen filaye. Wasu na cewa wai ƙwacen filaye ake yi, ta yaya za ka ƙwace filaye alhali kai ne ke da iko da filayen? ni nake da iko filaye a Abuja, to ta yaya zan ƙwace abun da nake da iko a kai?”

Ya ƙara da cewa yanzu ba kamar Rivers ba, da ƴan Najeriya baki ɗaya yake aiki, wanda hakan ya sa ƙara fahimtar wasu abubuwa.

“Wasu suna tunanin don ba a yi amfani da doka ba a baya, babu wanda zai zo ya yi. Amma ba haka ba ne, don wata gwamnati ba ta yi ba, hakan ba ya nufin babu gwamnatin ba za ta zo ta gyara. Don haka duk farfagandar da za a yi, ba za ta hana ni yin abubuwan da suka dace ba.”

legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp