Masu gadin teku a Amurka sun ce ta yiwu mutane shidan nan da har yanzu ba a gano su ba lokacin da jirgin ruwan dakon kaya ya daki gadar birnin Baltimore sun rasu.
Da yake jawabi ga manema labarai, Rear Admiral Shannon Gilreath, ya ce ba lallai mutanen su kasance a raye ba saboda tsawon lokacin da suka ɓata da kuma rashin kyawun yanayin ruwan.
Wakilin BBC ya ce hukumomi na ta aiki ba kaƙƙautawa, da jirage masu saukar ungulu da kwale-kwale da masu ninkaya, jami’ai sun bayyana yadda suke aiki cikin wahala saboda zurfin ruwan.
A ɓangare guda kuma hukumomin tashar ruwan Singapore da jirgin da ya taso daga can, sun ce a bara sau biyu ana duba lafiyarsa.