Jam’iyyar African Democratic Congress wato ADC, ta soki Shugaba, Boa Tinubu, bisa abin da ta bayyana “ɓacewar kwana biyar ba tare da bayani ba” bayan ya halarci taron BRICS na 2025 a ƙasar Brazil.
Tinubu wanda ya halarci taron a birnin Rio de Janeiro da ke Brazil, ya koma ƙasar a ranar Lahadi, kwana biyar da kammala taron.
A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce babu wani bayani a hukumance da aka fitar game da kwana biyar ɗin da aka yi shugaban bai koma ba bayan kammala taron.
“ADC na ƙalubalantar Bola Tinubu ya bayyana wa ƴan Najeriya ina ya tsaya ya yi kwana biyar bayan kammala taron BRICS a Brazil,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Bayan kammala taron a ranar Litinin 7 ga watan Yuli, sauran shugabannin ƙasashen da suka halarta sun koma ƙasashensu, inda suka yi wa ƴan ƙasarsu bayanin abin da ya faru a can, sannan suka koma bakin aiki.
“Amma shugaban ƙasarmu fa? sai a ranar Lahadi 13 ga watan Yuli muka gan shi, kuma ba tare da wani bayanin me ya sa ya yi jinkirin dawowa ba.”
Bolaji ya ce kwana biyar na da matuƙar muhimmancin ganin yadda Najeriya ke fama da matsalar rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.