Tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan mulki, yana mai neman ‘yan ƙasar su goya wa gwamnatin jam’iyyarsu ta APC baya “don ta yi nasara wajen gina ƙasa”.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban ya wallafa a shafukan zumunta, Buhari ya kuma nemi ‘yan Najeriya “su saka wa gwamnatin ta Tinubu albarka” kuma “su ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa”.
“Haka nan, Buhari ya yi wa gwamnatin Tinubu fatan gama mulki cikin nasara,” in ji Garba Shehu.
A yau Laraba 29 ga watan Mayu Tinubu ke cika shekara ɗaya da shan rantsuwar kama mulki bayan ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairun 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Muhammadu Buhari ne shugaban ƙasar da ya fara cin zaɓe a APC, inda ya mulki ƙasar daga 2015 zuwa 2023.