Peter Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, yayi kira da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus saboda gazawarsa wajen kai jam’iyyar zuwa mataki na gaba.
Fayose ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya taya zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu murnar nasarar da ya samu.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a safiyar Larabar da ta gabata ya ayyana Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Tinubu ya doke Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour inda ya zama wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Fayose ya ce, “Game da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ina kira da ya gaggauta yin murabus saboda gazawarsa wajen ciyar da jam’iyyar gaba.
A baya Fayosed ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Ina taya Asiwaju Bola Tinubu murnar zabar sa a matsayin shugaban kasar Najeriya. Ina kira ga sauran ’yan takara musamman Atiku Abubakar da su amince da sakamakon da aka samu domin amfanin kasarmu baki daya. Ko da yaushe za a sami wata rana.”