Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar Mauludin Nabiy, ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.,,
Tinubu ya jinjinawa mabiya addinin Musulunci a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shi shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ya fitar.
Ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen zurfafa tunani da tunawa da kyawawan halaye da karantarwar Manzon Allah.
“Yayin da muke bikin Mauludi, ya kamata mu yi tunani a kan irin rayuwar da Annabi Muhammad ya yi, wanda ya nuna tsafta, rashin son kai, juriya, kyautatawa da tausayi. Dole ne mu yi ƙoƙari mu ɓata waɗannan kyawawan halaye, ”in ji shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su sadaukar da ranar Mauludi domin yi wa kasa addu’a da kuma tausayawa juna.