fidelitybank

Ina taya Musulami murnar Maulidi – Gwamnan Bayelsa

Date:

Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya taya al’ummar musulmin jihar da ma fadin kasar nan murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Mista Daniel Alabrah ya fitar, ya bayyana cewa bikin Eid-el-Maulud bikin soyayya ne kuma lokaci ne na yin tunani a kan koyarwar Manzon Allah a kan hadin kai, tausayi da zaman lafiya.

Ya kuma umarci mabiya addinin Musulunci a jihar da su kasance masu kokarin zama masu rike da ‘yan uwansu, da nuna soyayya ta zahiri da tabbatar da zaman lafiya da sauran jama’a.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A wannan lokaci mai albarka na gudanar da bukukuwan sallar Eid-el-Maulud, ina taya ’yan uwana musulmi murnar zagayowar wannan rana da kuma fadin Nijeriya.

“Yayin da kuke murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad, kuma lokaci ne na yin tunani a kan manyan manufofinsa da koyarwarsa kan soyayya, hadin kai. tausayi da zaman lafiya.

“Ina kira ga masu bin addini da su nuna soyayya mai amfani, kishin kasa da tabbatar da zaman lafiya da sauran mutane. Ka’idodin kyakkyawar makwabtaka da kasancewa mai kula da ‘yan’uwa sun fi bayyana a lokacin kamar wannan.

“Bayelsa ta kasance gida ga kowa. Jiha ce da, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada, kowa yana gudanar da addininsa cikin ’yanci ba tare da tsangwama ko bari ba. Kuma gwamnatinmu ta kasance da tsayin daka wajen Æ™arfafa ’yancin yin ibada da tarayya.

“Yayinda zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba ke gabatowa, mu guji duk wani nau’in tashin hankali, mu ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da ake samu a jihar.

“Allah ya sa wannan bukin Idi ya kawo farin ciki da farin ciki a gare ku duka da jihar mu.”

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka Æ´an Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar HaÉ—in kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran Æ™asa za ka mayar da kai ba zaÉ“en 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp