Jagoran adawa Atiku Abubakar, ya aike da saƙon taya murna ga ɗan takarar shugaban ƙasar na NDC mai hamayya a Ghana, John Dramani Mahama, kan nasarar da ya samu a zaɓen ƙasar.
Hakan na zuwa ne bayan ɗan takarar jam’iyyar NPP mai mulki Mahamudu Bawamia ya amince da shan kaye tare da taya Mahama murna.
“Ina miƙa sakon taya murna kan nasarar da ka samu, mai girma zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana John Mahama,” in ji Atiku
Har yanzu dai hukumar zaɓen ƙasar ba ta fara bayyana sakamakon zaɓen a hukumance ba.