Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya mika sakon taya murna ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa cikarsa shekaru 82 da haihuwa.
Atiku wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X, ya na mai cewa da shi da iyalansa na taya Muhammadu Buhari murnar haihuwarsa na cika shekaru 82 a duniya.
Ya kuma yi masa addu’ar samun kosashen lafiya tare da samun wasu shekarun a nan gaba.