fidelitybank

Ina tare da ɗalibai masu sanya Hijabi – Gwamnan Kwara

Date:

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana cewa, ko shakka babu ya na tare da ɗalibai mata Musulmai kan lamarin sanya Hijabi cikin makarantun jihar.

Gwamnan Ya ce, wannan ita ce matsayarsa, saboda shari’o’in da kotu ta yanke kan lamarin da kuma kasancewar Kwara jiha ce mai daidaito tsakanin addinai, kuma jihar da tafi kama da Kudu wajen adadin masu addinai mabananta.

Abdulrazaq ya kuma ce, gwamnatinsa kawai doka da gaskiya take bi da kuma nuna adalci tsakanin kowa, a tabakin sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, wanda ya bayyanawa Daily Trust.

Wannan jawabi na Gwamna ya biyo bayan tuhume-tuhumen da Musulmai da Kirista ke yi, cewa Gwamnan ya ki bayyana ra’ayinsa kan lamarin saboda siyasa.

Tuni dai iyalan Habeeb Idris, ɗalibar da aka kashe yayin zanga-zanga a makarantar Oyun Baptsit kwanakin baya, sun yi watsi da diyyar Naira miliyan 1 da gwamnatin jihar ta basu. Hakazalika mutum 11 da suka jikkata sun yi watsi da kuɗi Naira 250,000 da gwamnatin jihar ta basu.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...

Alhazai Miliyan Ɗaya da Rabi ke tsayuwar Arfa

Dubun dubatar alhazai daga sassan duniya na hawan Arafa...

Sarkin Kano na 15 ya dakatar da yin hawan Sallah

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado...

Maniyacin jihar Kano da yake kokarin zama Alhaji ya rasu a Saudiyya

Daya daga cikin alhazan jihar Kano, Shu’aibu Jibrin, an...

Tinubu ya bayar da tallafin Biliyan Biyu da Tirela 20 na Shinkafa ga al’ummar Mokwa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce, shugaban ƙasar...

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga...

An samu gawar mutane 7 a ambaliyar Neja

Rahotonni na cewa masu aikin ceto sun zaƙulo gawar...
X whatsapp