fidelitybank

Ina takaici yadda wasu Matan ke shiga shaye-shaye a Kano – Sarki

Date:

Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya karbi bakuncin shugabar kungiyar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Ambasada Maryam Hassan a fadar sa.

Sarkin ya bayyana damuwarsa kan yadda shaye-shayen miyagun kwayoyi ke karuwa, musamman a tsakanin mata da matasa a cikin al’umma.

“Wasu daga cikin batutuwan da aka gabatar a gabanmu na da alaka da shaye-shayen miyagun kwayoyi; akwai ayyukan da ba za a iya aiwatarwa ba tare da shan kwayoyi ba, kamar mutum ya kashe dan uwansa ko iyayensa. Duk wannan ba zai iya faruwa ba sai idan mutum ya rasa hayyacinsa”. Ya kara da cewa

Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bukace su da su mayar da hankali wajen wayar da kan al’umma, musamman kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi da ya zama ruwan dare gama gari.

A nata jawabin, shugabar kungiyar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Ambasada Maryam Hassan, ta bayyana cewa sun zo ne domin sanar da mai martaba irin ayyukan kungiyar musamman yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin al’umma musamman mata da matasa.

Ta ce, “Muna shirya taron karawa juna sani ga malamai da masu rike da mukaman gargajiya domin wayar da kan jama’a. Mun kuma gabatar da wata doka kan shaye-shayen miyagun kwayoyi ga Majalisar Dokoki ta kasa, amma har yanzu ba a gabatar da ita ba. Muna neman goyon bayan masarautar Kano don ganin an amince da kudirin a majalisar dokokin kasar.”

Bayan haka, Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya nada sabon Hakimin Kutama a karamar hukumar Gwarzo, Muhammad Murtala Safiyanu.

the sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp