fidelitybank

Ina takaici bisa yadda yunwa ke kashe ƴan Najeriya – Peter Obi

Date:

Kusan yara 40 ne suka mutu a wani hatsari yayin wani taron liyafar yara da aka shirya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar Laraba.

Haka zalika, a ranar Asabar, wani turmutsutsin ya faru a rabon tallafin a cocin Holy Trinity Catholic Church da ke unguwar Maitama a Abuja, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 tare da jikkatar wasu da dama.

A jihar Anambra, rahotanni sun bayyana cewa mutane kusan 17 a garin Okija yayin wani hatsari da ya faru a kokarin samun kayan tallafi.

Da yake tsokaci kan lamarin Obi ya bayyana takaicinsa a wata sanarwa da ya fitar ta dandalin sada zumunta na X. Ya ce hatsarurrukan sun nuna gazawar tsarin shugabanci da ke addabar Najeriya.

“Na yi matuƙar bakin ciki da damuwa kan asarar rayuka yayin neman abincin da zasu ci”

Obi ya yaba da ƙoƙarin masu shirya tarukan don tallafa wa talakawa amma ya bayyana cewa rashin ingantaccen tsarin tattalin arziki da shugabancin kasa ya sanya mutane cikin yanayin da ke jefa rayukansu cikin haɗari.

“Ya kamata a tambayi yadda ƙasa mai albarkatu irin Najeriya ta gagara ciyar da al’ummarta, duk da arzikin filayen noma da muke da su,” in ji shi.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda hatsarurrukan suka shafa. Obi ya ce, “ina mika ta’aziya ta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a Oyo, Anambra, da Abuja kuma ina fatan waɗanda suka jikkata su samu sauƙi cikin gaggawa.”

punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp