Wata matashiya ‘yar Jihar Ekiti a kudancin Najeriya mai suna Damilola Adeparusi, na can tana yunƙurin kafa tarihi na mafi daɗewa tana yin girki a duniya, inda take son cimma awa 120.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Adeparusi, wadda ɗalibar Jami’ar Tarayya ta Oye-Ekiti ce, tuni ta yi girki na awa 56 ya zuwa safiyar Lahadi a Ilupeju-Ekiti.
Tana girka sanwar ce a wani gida a Ƙaramar Hukumar Oye, kuma ta fara ne da ƙarfe 12:00 na dare a ranar Alhamis (Juma’a 9 ga watan Yuni), amma a wani ƙaramin wuri da babu iska sosai.
Matashiyar na ƙoƙarin zarta Hilda Baci ne, wadda ta ce ta yi girkin awa 100 a Jihar Legas da zimmar shiga kundin tarihi na Guinness World Record. Sai dai Guinness sun ce suna aikin tantance gaskiyar iƙirarin nata tukunna.
Baya ga kasancewarta mai girki, Adeparusi marubuciyar waƙar zube ce, a cewar NAN.