Dan kasar New Zealand da Nigeria, Israel Adesanya, ya bayyana Najeriya a matsayin “wuri mai cin hanci da rashawa”.
Ya ce yana son yan Najeriya, amma akwai jajayen tutoci da yawa game da kasar.
Karanta Wannan: Na jinjina wa Adesanya bisa nasarar da ya samu – Tinubu
Adesanya ya yi nuni da cewa, shugabannin Najeriya na da burin wawure dukiyar al’umma.
Ya ce, “Najeriya wuri ne na cin hanci da rashawa. Ina son jama’ata amma gwamnati ce kawai; kowa na kokarin nemo hanyar da zai saci kudi.”
Ku tuna cewa Israel Adesanya ya ɗaga tutar Najeriya, yayin da ya doke abokin hamayyarsa Alex Pereira a wasan dambe na UFC 287 a ranar 9 ga Afrilu, 2023, don maido da kambunsa na matsakaicin nauyi.
An biya shi dala miliyan 3.18 don yakin da ya yi da dan kasar Brazil, abin da ya sa ya zama dan wasan UFC mafi yawan albashi na uku a halin yanzu, bayan Conor McGregor da Jon Jones.
Ita ce mafi girman biyan kuɗinsa.