Zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu, ya buƙaci ‘yan ƙasa da su haɗa-kai wajen aiki tare a wani jawabi da ya yi wa magoya bayansa bayan sanar da shi a matsayin wanda ya samu nasarar zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar.
Tsohon gwamnan na Legas ya ce, yana son ya yi aiki tukuru wajen ci gaban Najeriya.
Tinubu na jam’iyya mai mulki ta APC ya samu kuri’u kusan miliyan tara, inda ya doke sauran ‘yan takara.
Magoya bayan jam’iyyar na ta shagul-gula a sassa daban-daban na ƙasar.
Mista Tinubu zai karɓi mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari wanda wa’adin mulkinsa karo na biyu ke ɗab da karewa.