A ranar Alhamis din da ta gabata ne tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bukaci babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta mayar da shari’arsa da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC zuwa Kogi.
Da yake magana ta bakin lauyansa, Adeola Adedipe, Bello ya shaida wa kotun a ranar Alhamis cewa, tun da aka zarge shi da aikata laifin a lokacin da yake gwamnan jihar Kogi, ya dace a gudanar da shari’ar a jihar, inji rahoton TVC.
Hukumar EFCC dai ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a gaban kotu bisa zargin almundahanar Naira biliyan 82 a gaban kotun mai shari’a Nwite.
Idan dai za a iya tunawa dai sau hudu tsohon gwamnan ya ki bayyana a gaban kotu, bisa dalilai daban-daban, kamar yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta nuna masa son zuciya.
Har yanzu ba a san inda tsohon gwamnan yake ba tun bayan da jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa suka yi yunkurin kama shi daga gidansa da ke Abuja.