Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin gina ƙasa da za ta tabbatar da daidaito da adalci da kuma rage giɓin da ke tsakanin al’umma.
Ya ce ko da yake ya yi imani masu kuɗi su ci moriyar dukiyar da suka mallaka da guminsu, amma jazaman ne duk wani ɗan Najeriya mai aiki tuƙuru ya samu damar da zai ci gaba a rayuwa.
Shugaba Tinubu na wannan bayani ne a cikin jawabin da ya gabatar na shiga sabuwar shekara ta 2024.
Ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki ba kama hannun yaro don tabbatar da ganin duk ‘yan Najeriya sun ɗanɗani daɗin gwamnatinsu.
Tinubu ya ce abin murna sosai yi wa al’ummar ƙasar maraba da shiga sabuwar shekara ta 2024, kuma dole ne su ɗaga hannu don yi wa Allah godiya da wannan karimci da baiwa da ya yi wa Najeriya da kuma rayukan al’ummarta.
Ya ce a tsawon wata bakwai da ya shafe a kan mulki, ya ɗauki wasu matakai da suka wajaba kuma masu wahala don ceto ƙasar daga shiga bala’in tattalin arziƙi, daga ciki akwai batun cire tallafin man fetur da dunƙule tsarin canza kuɗaɗen ƙasashen waje, da ke amfanar masu kuɗi kawai
Shugaba Tinubu ya ce yana sane da cewa a lokuta da dama hirarraki da muhawarorin jama’ar Najeriya na mayar da hankali ne a kan batutuwan tsadar rayuwa da matsanancin hauhawar farashi wanda a yanzu ya kai kashi 28% da kuma yawan marasa aikin da ba za a amince da shi ba.