Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasar Najeriya na 2023, Atiku Abubakar, ya buƙaci kotun ƙolin ƙasar ta ba shi damar miƙa sabbin hujjoji a ci gaba da matakinsa na ƙalubalantar nasarar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Wata buƙata da lauyoyinsa suka gabatar, ta ce sabuwar shaidar da Atiku ke son gabatar wa kotun za ta tabbatar da zargin da yake yi kan cewa shugaba Tinubu ya yi amfani da takardun bogi a lokacin da yake ƙoƙarin ganin ya fafata a zaɓen shugaban ƙasa.
Atiku Abubakar ya ce wannan abu da Tinubu ya yi na nuna cewa ya aikata laifuka biyu, wato ƙirƙirar takardar kammala karatu ta bogi da kuma ƙarya.
A cewar Atiku waɗannan hujjoji sun ishi kotun ƙoli ta dogara da su wajen cire shugaban ƙasar daga muƙaminsa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar na so ne kotu ta ba shi wannan dama domin ya miƙa mata takardun shaidar kammala karatun Bola Ahmed Tinubu, waɗanda jami’ar jihar Chicago da ke Amurka ta miƙa masa a ranar biyu ga watan Oktoba.
Bayanai dai sun nuna cewa Atiku ya shigar da buƙatar tasa ce a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sai dai har yanzu kotun ba ta sa ranar da za ta yanke hukunci kan buƙatar ta Atiku ba.
Shi dai Atiku Abubakar yana ƙalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu ne ya samu a zaɓen shugaban Najeriya da aka gudanar cikin watan Fabarairun 2013.
A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar Tinubu tare da yin watsi da hujjojin Atiku Abubakar na ja