Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Allison-Madueke, ta roki ‘yan Najeriya da su yi mata addu’a kan zarge-zargen da ake yi mata na cin hanci da rashawa da kuma zargin cin hanci da rashawa da Hukumar Yaki da Laifuka ta Burtaniya NCA ta yi mata.
“Ina bukatan addu’a. Don Allah a yi mini addu’a,” kamar yadda ta shaida wa ’yan Najeriya mazauna Birtaniya bayan kammala zaman kotun da ke hawa na biyar.
Wani babban Lauyan da ya taso daga Najeriya domin ya wakilci wanda yake karewa, Benedict Peters, ya ce bayan sauraron karar “harka ta yi rauni,” kuma ba za ta tashi ba.
Da yake magana da ‘yan jarida a gaban kotun, Emeka Ozoani (SAN) ya bayar da hujjar cewa “su, NCA, sun shafe shekaru biyar zuwa shida suna bincike kan lamarin kuma suna kokarin tabbatar da abin da suka yi da kudaden masu biyan haraji.
“Na zo ne don wakiltar ɗaya daga cikin waɗanda ke da alaƙa da shari’ar.”
Da aka tambaye shi ko ya taso ne daga Najeriya domin sauraren karar. Ya ce: “E. Na zo ne saboda abokiyar cinikina.”