Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce, ya nemi shawara dafa tsohon kocin Gunners Arsene Wnger kan yadda zai iya lashe gasar Premier gabanin wasan hamayyar arewacin Landan da Tottenham Hotspur.
Kungiyar ta Arteta na saon kawo ƙarshen shekaru 20 da suka kawashe ba tare da cin wannan kofin ba, kofin ƙarshe da Arsenal ta ci shi ne na 2003-04 da Wenger ya ɗauka cikin uku da ya ci wa ƙungiyar.
Za su je wasan Tottenham ne da maki ɗaya tsakaninsu da Manchester City da ke matsayi na biyu a gasar.
“Na tattauna da shi na wasu lokuta kaɗan,” in ji Arteta, wanda ya yi wasa na shekara biyar ƙarƙashin Wenger lokacin da yake daf da ajiye takalmansa.
“Akwai wasu maudu’ai kan yadda suka lashe gasar a baya kuma daga baya suka ƙara.”
Arsenal na da damar ba da maki hudu tsakaninta da City da za ta fafata da Notthengham Forest an jima da maraice.