Gwamnan jihar Osun, ya musanta rahotonnin da ke cewa ya fice daga jam’iyyar PDP mai adawa a Ć™asar zuwa APC mai mulki.
Ademola Adeleke ya jaddada biyayyarsa ga PDP tare da tabbatar wa kwantar wa da baya hankali, kamar yadda mai magana da yawunsa Mallam Olawale Rasheed ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Asabar.
“Ina tabbatar wa mazauna jihar Osun cewa har yanzu ina nan daram a PDP, ba zan koma wata jam’iyya ba,” a cewar gwamnan.
A ranar Laraba ne wasu jiga-jigai na jam’iyyar ta PDP suka sanar da shiga jam’iyyar haÉ—aka ta ADC domin Ć™alubalantar Shugaba Tinubu na APC a zaÉ“en 2027.
Cikin manyan ‘yan PDP É—in har da Atiku Abubakar, É—antakararta na shugaban Ć™asa a 2023, da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, da tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido, da sauransu.