Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya ce, zai ci gaba da zama a jam’iyyar PDP amma ya kawar da yiwuwar marawa da kuma yin aiki domin samun nasarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.
Wani makusancin gwamnan ya shaidawa manema labarai a yau, 28 ga watan Yuli cewa ba zai koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba, duk da ci gaban da shugabannin jam’iyyar ke samu gabanin babban zaben 2023.
Gwamna Wike ya yi shiru kan zaben shugaban kasa da ke tafe biyo bayan koke-kokensa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku.
Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Wike ya yi barazanar bayyana wa ‘yan Najeriya duk wani abu da ya faru a jam’iyyar PDP tun bayan fitowar Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Wike ya ce: “Akan Atiku, zan yi magana nan ba da jimawa ba, kuma ‘yan Najeriya za su san gaskiyar duk abin da ya faru a PDP a ‘yan kwanakin nan.”
Sai dai Atiku ya ce kwamitin da gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya jagoranta ya ba shi sunaye guda uku kawai ya yanke shawarar zabar wadanda zai yi aiki da su.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa.