Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya karyata rade-radin da ake yadawa a jihar cewa, ya yi murabus daga mukaminsa.
Baba Tela yana mayar da martani ne a kan wasu labaran da aka wallafa a shafukan sada zumunta cewa, ya ajiye mukaminsa na mataimakin gwamnan jihar Bauchi.
A cewarsa, har yanzu yana kan mukamin mataimakin gwamnan jihar Bauchi.”
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na ofishin mataimakin gwamna Sani Mu’azu Ilellah ya raba wa manema labarai a Bauchi.
“An jawo hankalin mataimakin gwamnan jihar Bauchi Sen. Baba Tela kan labaran karya a shafukan sada zumunta cewa, mataimakin gwamnan ya yi murabus daga mukaminsa. Bayanin rahoton da ake yi a kafafen sada zumunta na zamani, kwatankwacin tunanin marubuci ne.”
“Don kauce wa shakku, muna so mu tabbatar wa al’ummar Jihar Bauchi masu son zaman lafiya da himma, musamman ma kasa baki daya, cewa Sanata Bala Tela bai yi murabus daga mukaminsa na Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi ba.”
“Mai girma mataimakin gwamna, ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da manufofi da manufofin gwamnatin jihar Bauchi a karkashin ingantacciyar jagorancin mai girma Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.” Sanarwar ta kara da cewa a sassa daban-daban.
Yayin da yake jaddada goyon bayansa da biyayya ga gwamnan, Baba Tela ya gargadi masu yada jita-jita da ke da niyyar haddasa rashin jituwa a jihar da su guji irin wannan aika aika.