Shugaban Bola Ahmed Tinubu, ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon ma’aikacin gidan radiyon Muryar Amurka, Kabiru Usman Fagge wanda ya rasu ranar Juma’a a Amurka.
Marigayin mai shekara 77 a duniya, ya yi shuhuna tsakanin al’ummar Hausawa a faÉ—in duniya saboda aikin da ya yi da gidan radiyon Muryar Amurka na kimanin shekara 25.
Cikin wata sanarwar saÆ™on ta’aziyyar da Tinubu ya fitar, ya jinjina wa marigayin saboda ”taimakawar da ya yi wajen gina Æ™asa da kuma taimakon da ya bai wa fannin ilimi”, musamman cikin fitaccen shirin da yake gabatarwa na ”Ilimi Garkuwar Dan’adam’ a kowanne mako.
“Muna jinjina masa kan yadda ya zaÉ“i aikin da yake son yi kuma ya haska Æ™imar Najeriya a idon duniya,” in ji sanarwar.
Tinubu ya miÆ™a ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da sauran É—aukacin al’umar Najeriya da na duniya baki É—aya.