Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana takaicinsa kan yawan tashin hankula da ake samu tsakanin magoya bayan jam’iyyun siyasa a jihar.
Wata sanarwa ta hannun mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labaru, Isa Gusau, ta ce an fi samun rikicin ne tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da kuma na PDP mai hamayya.
Gwamnan ya buƙaci kwamishinan ƴan sanda na jihar ya gudanar da bincike kan rikice-rikice da aka samu na baya-bayan nan tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.
Ya kuma buƙaci ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki, da ƴan takara su tabbatar sun kauce wa rigingimu a lokutan yaƙin neman zaɓe domin kauce wa shiga hannun hukuma.