Shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Ado Alhassan Doguwa da aka ruwaito sun yi artabu da dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a jam’iyyar All Peoples Congress, Murtala Sule Garo, ya bukaci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya dauki cikakken shugabancin jam’iyyar tare da ceto ta daga masu son ruguza ta idan jam’iyyar za ta ci zabe a 2023.
An samu labarin musayar kalamai tsakanin shugaban majalisar da dan takarar mataimakin gwamna a yayin taron masu ruwa da tsaki a gidan dan takarar gwamna na jam’iyyar, Nasiru Yusuf Gawuna, a ranar Lahadi, 30 ga Oktoba, 2022.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, 31 ga watan Oktoba, Ado Alhassan Doguwa, ya ce: “Ina matukar girmama Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo kuma ina fatan ganin sun zama Gwamna da Mataimakin Gwamnan Jihar mu mai albarka”.
Ya ci gaba da cewa: “A rubuce yake cewa babu inda na taba raina Sule Garo ko kuma na kira sunansa, amma a lokuta da dama ya saba kulla makirci na, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kamar yadda aka nuna kwanan nan. lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mu, Sanata Ahmad Bola Tinubu ya zo Kano”.
Doguwa ya kara da cewa: “Lokacin da Tinubu ya shirya zuwa Kano na gyara allunan talla, kusan guda goma a wurare masu muhimmanci, ina maraba da shi, amma a daren da na kafa allunan, wasu ‘yan iska sun yi kaca-kaca da sunan Garo suna lalata komai. Duk da haka, ban tunkare shi ba, ban kuma yi masa magana a kai ba”.
Dangane da rahotannin da ke cewa ya kai wa Murtala Sule Garo hari a yayin taron jam’iyyar APC, ya yi watsi da shi da cewa “ba komai ba ne illa yaudara da zagon kasa” da aka yi masa domin babu wani abu makamancin haka.
“Abin da ya faru shi ne na kira shugaban jam’iyyar ina son ganin sa, sai ya ce in je gidan Gawuna inda suke taro. Da isowar wurin a cikin kayana na Sardauna Rano, kai tsaye na nufi dakin da suke na yi magana da shugaban jam’iyyar. Sai dai kamar yadda ya saba, Murtala Sule Garo cikin zagi ya ce in tafi. Ko da na ce masa na zo ne don ganin Chairman, sai ya ci gaba da zagina har sai da naji na mayar da martani,” ya bayyana.
Garo, ya yi ikirarin cewa ya garzaya ne ya buge shi kuma a haka ne ya fado kan teburi dauke da kofi ya raunata kansa. “Ban taba kai masa hari ba kamar yadda ake ruwaito,” in ji shi.
Da yake takaita matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar APC a jihar, Doguwa ya yi gargadin cewa lokaci ya yi da Gwamna Ganduje ya amince da daukar nauyin al’amuran jam’iyyar idan ba haka ba rigimar na iya kawo cikas ga jam’iyyar a babban zabe mai zuwa.