Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi kira ga kafatanin shugabannin jam’iyyar APC su hada kai da juna, domin ganin Asiwaju Bola Tinibu, ya samu nasarar zama shugaban kasa.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Babajide, ya bayyana hakan ne a yayin kai ziyarar duba aiki karamar hukumar Amuwo-Odofin fa karamar hukumar Oriade ranar Laraba.
A cewarsa, akwai bukatar su sadaukar da kansu, domin Tinubu ya zauna daram-dam a Abuja, domin mulki ta dawo hannun yankin Legas.
Ya ce: “Ina kira gareku wannan gwagwarmaya da muka dauka na ganin cewa, Asiwaju (Tinubu) ya wakilcemu a Abuja na nan tafe. Ina kira ga dukkan Sarakuanan gargajiya su hada kai da gwamnonin kananan hukumomi . Ina kira ga dukkan al’ummar Inyamurai, Kudu da Arewa mu mara masa baya”. In ji Babatunde.