fidelitybank

Ina kan baka ta a zaben 2023 – Buhari

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari ya nanata kudurinsa na tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe a kasar a 2023.

Shugaban ya fadi hakan ne a jawabin bankwana da ya yi a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi birnin New York na Amurka.

”A matsayina na Shugaba, daya daga cikin tarihin da nake son bari shi ne na ga cewa an gudanar da sahihi kuma tsabtataccen zabe. Ta hakan ne ‘yan Najeriya za su zabi shugabannin da suke so,” in ji Buhari.

Ya kara da cewa wanda duk zai gaje shi zai gudanar da jawabi a madadin Najeriya a taron majalisar na gaba.

”A yanzu muna shirin gudanar da babban zabe a Najeriya a watan Fabrairun badi. Saboda haka a taron Majalisar Dinkin Duniya na 78, za ku ga sabuwar fuska ne a kan wannan munbari”, a cewar Shugaba Buhari.

Ya kuma yi magana a kan rawar da kasarsa ta taka wurin ganin an mika mulki salun alun a wata gwamnatin dimokradiyya a Gambia.

Shugaban zai kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu a watan Mayun badi, inda zai mika mulki ga sabuwar gwamnati.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp